Jami’an tsaro sun rufe manyan tituna a birin Omdurman domin hana masu zanga-zanga isa manyan gine-ginen gwamnatin,
An ranar 25 ga watan Oktoba ne aka yi wa Fira ministan kasar daurin talala a gida , kafin daga bisani ya koma aiki a ranar 21 ga watan Nuwamba bayan da suka kulla yarjejeniya da shugaban soji na kasar Janaral Abdel Fattah Al-burhan
Dubban mutanen kasar ne suka ci gaba da gudanar da zanga- zanga a kan titunan manyan biranen kasar duk da mataken tsaro da aka dauka, kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 57 tare da jikkata wasu Daruruwa daga lokacin da aka kifar da gwamnatin rikon kwaryar kasar.
342/